Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Facebook Ya Rufe Wasu Shafuka 800 Kan Yada Labarun Karya


Kamfanin sada zumunta na Facebook ya sanar da cewa ya goge wasu shafuka sama da 800, wadanda yawancinsu a Amurka suke, kuma suna yada labarun karya da suka shafi siyasa.

Sai dai kamfanin na Facebook yayi watsi da bukatar da Muryar Amurka ta mika masa na cewa ya bayyana sunayen shafuka 559 da sunayen wasu 251.

Jaridar Washinton Post ta bayyana Shafin ‘Nation in Distress’, na magoya bayan shugaban kasa Donald Trump na daga cikin shafukan da aka goge, kuma shafin yana da magoya baya sama da miliyan 3.

Kamfanin Facebook ya ce yawancin shafukan da aka sauke, suna yaudarar mutane ne da labaran karya domin mutane su danna su shiga shafukansu na yanar gizo.

A baya dai, Facebook ya goge shafukan da ake yada labaran ‘karya da aka kirkiresu daga kasashen Iran da Rasha, kasashen dake adawa da Amurka. Kamfanin dai yace yawancin shafukan da ya goge a wannan lokacin duk an kirkiresu a nan Amurka ne.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG