Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fadar Shugaban Rasha Tayi Tur da Hukumomin Leken Asiri Na Amurka


Shugaban Rasha Vladimir Putin
Shugaban Rasha Vladimir Putin

Fadar shugaban Rasha ta Kremlin tana Allah wadai da cewa zargin da hukumomin leken asirin Amurka suke yiwa kasar cewa tayi shishshigi cikin harkokin zaben Amurka da zummar taimakawa Donald Trump, a zaman wanda bashi da tushe kuma tamkar wasan yara ne ko rashin kwarewa.

Kakakin fadar Kremlin Dmitry Peskov, ya fada jiya Litinin cewa, "wadannan zarge-zarge marasa tushe wadda ba'a bada wata shaida ba, da aka gudanar da rashin kwarewa,da fushi bai ma dace a dangantashi da wata sananniyar hukumar leken asiri ta duniya ba.

Sanarwar ta ci gaba da cewa "mun fara gajiya da wadannan zarge zarge" inji Peskov.

Kalamansa sune na farko daga fadar shugaban na Rasha tun bayanda hukumomin leken asirin Amurka suka fito da rahoto ranar Jumma'a data wuce, inda suka bayyana kwarin gwuiwa cewa shugaban Rasha Vladimir Putin da kansa ya bada umarnin a gudanar da kamfen na gurgunta harkokin zaben Amurka.

Ahalinda ake ciki kuma, jiya Litinin Amurka ta kakabawa babban jami'i mai gudanar da bincike a fadar Kremlin Alexander Bastrykin, da jami'ai a fadar shugaban Rashan su hudu. Bisa dalilai da ma'aikatar harkoki wajen Amurka ta kira 'ayyuka na mummunar ketan hakkin Bil'Adama".

XS
SM
MD
LG