Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fadar White House Ta Maidawa Acosta Izinin Daukar Labari A Fadar


Dan jaridar CNN, Jim Acosta
Dan jaridar CNN, Jim Acosta

Fadar shugaban Amurka ta White House ta mayarwa dan jaridar gidan talabijin na CNN Jim Acosta izinin daukar labarai a fadar, tana mai gargadinsa da cewa zai iya rasawa idan har yaki bin umarnin daukar labarai a fadar.

White House dai ta janye izinin Acosta ne bayan wata sa’insa da ya yi da shugaban kasa Donald Trump, a lokacin wani taron manema labarai makonni biyu da suka gabata.

CNN dai ta ce tunda fadar White House ta amince da mayarwa wakilinta izininsa, to zata janye karar da ta kai gwamnatin Trump.

Tun farko dai Acosta ya ki mika makirufo bayan da ya riga yayi tambayarsa, yana kokarin sake yin wata tambaya. A nan ne aka zargi Acosta da ture hannun wata ma’aikaciya da ta yi yunkurin karbar makirufo daga hannunsa, zargin da shi Acosta ya musanta.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG