Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Faransa Ta Farauto Wasu Bakin Haure 50 A Cikin Jirgin Ruwa


Bakin haure

Hukumomin Faransa sun ce wasu bakin haure guda hamsin da suka saci hanyar su a cikin wani jirgin ruwan Faransa a wani yunkurin shinga kasar Ingila daga birnin Dover, sun isa Calais mai tasahar jirgin ruwa a arewacin Faransa a jiya Asabar.

Jami’an sun ce an kama mutane 44 a cikin bakin hauren, lamarin da ya gurgunta yunkurin su na isa Ingila a cikin jirgin da yake komawa Ingila.

Mutane biyu a cikin bakin hauren sun fada a cikin ruwa amma dai an gaggauta ceto su.

Jami’an hukumar harkokin ruwan kasar Faransa sun ce an jinkirtar da jigilar jirgin ruwa na sa’o’I dama, yayin da ‘yan sanda suke gudanar da bincike a ciki jirgin.

Hukumomin sun ce akalla bakin haure guda dari suka je tashar jirgin ruwan da yammacin jiya Asabar.

Kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP, yace ‘yan sandan sun ci gaba da binciken jirgin ruwan har izuwa safiyar yau Lahadi kuma a cewar ‘yan sanda har yanzu akwai akalla bakin haure guda hudu dake boye a cikin jirgin ruwan da aka kamo sauran bakin hauren.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG