Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Amurka Zai Gana da Shugaban Koriya ta Kudu Yau Talata


Shugaban Amurka Donald Trump da Shugaban Koriya ta Kudu Moon Jae-in
Shugaban Amurka Donald Trump da Shugaban Koriya ta Kudu Moon Jae-in

Yayinda ake tababan yiwuwar taron koli tsakanin shugaban Amurka da na Koriya ta Arewa kamar yadda suka shirya zasu yi watan gobe, shugaban Koriya ta Kudu zai gana da Trump a Fadar White House yau Talata

Yayin da ake ta tantama kan yiwuwar samun nasarar taron kolin da za a yi tsakanin shugaban Amurka da na Korea ta Arewa da kuma kokwanton da ake nunawa kan ko taron zai yiwu kamar yadda aka tsara, a yau Talata shugaban Amurkan, Donald Trump zai gana da takwaran aikinsa na Korea ta Kudu a Fadar gwamntin White House.

Yayin ziyarar, ana sa ran, shugaba Moon Jae-in zai yi kokarin tabbatarwa Shugaba Trump cewa, ganawar da zai yi da shugaba Kim Jong Un za ta bude wani babi da zai kafa babban tarihi.

A cewar jami’ai a Amurka da ma kasashen waje, shugaba Trump na tuntubar hadimansa da shugabannin kasashen duniya, kan ko ya je Singapore domin haduwa da shugaba Kim.

Wasu jami’an gwamnati a Washington da suka nemi da kada a bayyana sunayensu, sun dora laifi akan jami’an Korea ta Kudu kan yadda suka zuzuta aniyyar shugaba Kim ta kwance damarar kera makaman nukiliya.

Wannan kuma wata mahanga ce da wasu ma da ke wajen gwamnatin ta Trump suka amince da ita.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG