Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Faransa Ta Kai Samamen Farko A Kan 'Yan Ta'adda A Kasar Mali


Mali France President
Mali France President

Ma'aikatar Tsaron Faransa ta ce ta kai wani hari na farko da jirgi mara matuki, da ya hallaka masu tsats-tsauran ra’ayin addinin Islama 7 a tsakiyar Mali a karshen makon da ya gabata.

Sojoji Faransa sun hada kai da rukunin sojoji na kasashe kadan da suka yi amfani da jirage marasa matuka dauke da makamai, a cikin su har da Amurka.

A cikin wata sanarwa jiya Litinin ta ce hari na jirgi mara matuki an kaishi ne a ranar Asabar a lokacin da shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron yake ziyara a makwabciyar kasar Ivory Coast, inda Faransa ta ke da sansanin sojanta.

Aikewa da jiragen marasa matuka yana zuwa ne wata daya bayan da jiragen Faransa masu saukar ungulu guda biyu suka yi karo a Mali, da ya kashe sojoji goma 13, wanda wannan shine adadi mafi yawa da sojojinta suka mutu a cikin kusan shekaru 40 da suka gabata.

Sojojin Faransa sun yi nasarar gwada makaminta na jirgi mara matuki dauke da makami karon farko a makon da ya gabata, kana Ministan Tsaron Faransa, Florence Parly, ta kira jiragen marasa matuka “Masu kariya ga dakarun su da kuma suke aiki akan makiyansu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG