Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

*Faransa Ta Tsawaita Kwangilar Corinne Diacre Zuwa 2024. *Diogo Jota Zai Kasance A Liverpool Har Nan Da Shekaru 5. *Karawar Rebecca Da Venus


Diogo Jota na Liverpool.
Diogo Jota na Liverpool.

Za mu soma labarun wassaninmu na ranar yau da mai koyar da kungiyar kwallon kafa ta mata ta kasar Faransa, Corinne Diacre, wadda a yau Talata ne hukumar kwallon kafa ta kasar Faransa ta bada sanarwar kara ma ta wa'adin kwangilarta har izuwa 2024. Wannan ko, domin halartar wassanin cin kofin duniya na mata da wassanin Olympic da Birnin Paris zai karbi jagoracinsa a 2024.
Ita dai Corine Diacre, ta kai kungiyar ta kwallon mata ta Faransa a karo na farko a tarihin ta, a wassan kusa da na karshe na cin kofin kasashen Turai na mata na kwallon kafa da ya kammala a makon jiya a Burtaniya, inda ta sha kashi a wasan kusa da na karshe a hannun Jamus da tayi mata ci 2 da 1.
-------------------------------------------------------------------------------------------------
A nasa bangaren mai cin kwallaye dan kasar Portugal wa club din Liverpool Diogo Jota, a yau ne kungiyar ta Burtaniya da ta karkare a matsayi na 2 a kakar kwallon da ta gabata a Ingila ta bada sanarwar cewa dan wasan ya rattaba hannu kan lokaci mai tsawo, wanda jaridun Ingila suka bada sanarwar zai kai har a 2027.
Kenan Diogo Jota, zai cigaba da bugawa club din Liverpool har tsawon shekaru 5 a nan gaba.
----------------------------------------------------------------------------------------------
Ita ko gasar kwallon kafa ta kasar Spain da a ke kira a yanzu la Liga, zata canza suna daga farkon shekara ta 2023/2024.
Dalili ko shine, Bankin da ke jaye da ragamar wasan mai su na Banque Santander, zai janye daga wannan kwangilar, inda kamfanin EA Sport, zai maye gurbinsa.
Wannan zai shigar wa hukumar kwallon kafa ta Spain kudade, daga miliyon 30 zuwa 40 na yuro a kowace shekara, maimakon rabin hakan da take samu a halin yanzu.
Shi dai kamfanin na EA Sport shi ne ke da wasannin FIFA Football da a ke iya lodi a salulinan android.
Venus Williams
Venus Williams
.................................................................................................
A wasannin Tennis na mata na kombalar Washington, yar kasar CANADA ce Rebecca Marino ta yi karin kwamallo da Venus Williams 'yar ajin 32, inda ta kakabike ta da ci 4 - 6, 6 - 1, 6 - 4.
Sama da shekara guda kenan kamin Venus Williams din ta shiga wata babbar kombala kamar irin wannan ta Washington.
Saurari cikakken rahoton Harouna Mammanne Bako:
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG