Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Farar Hula Da Yawa Sun Mutu a Wani Hari Da Aka Kai a Nijar


Wasu yan bindia sun kashe farar hula da yawa a jiya Asabar a Nijar, a cewar hukumomi, a wani hari na baya-baya da aka kai a yankin Tillaberi da ke yammacin kasar wanda ke fama da tashin hankali.

“Da misalin karfe 12 na rana aka kai harin kuma an samu mace-mace, abinda wani babban jami’i a yankin ya fadawa kamfanin dillancin labaran AFP kenan, ba tare da ya bada adadin wadanda harin ya shafa ba ko cikakken bayani akan farmakin.

Haka kuma wani jami’i shi ma ya ce an kashe farar hula da yawa a wani harin da aka kai a Tchamo-Bangou, wani kauye da ke kusa da iyakar kasar da Mali.

“Maharan sun je su zagaye kauyen ne suka kuma kashe har mutane 50. An kai wadanda suka jikkata asibitin gundumar Ouallam, a cewar wani dan jaridar gidan rediyon yankin wanda ya so a sakaya sunansa.”

Harin dai ya faru ne a ranar da aka fidda sakamakon zagayen farko na zaben shugaban kasa da aka yi a Nijar wanda ya nuna cewa dan takarar jam’iyya mai mulki Mohamed Bazoum shi ne ke kan gaba, yayin da kuma ake shirin yin zabe zagaye na biyu a wata mai zuwa.

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Gobara A Jihar New York

An Yi Jana'izar Mutane 15 Da Suka Mutu A Gobara A Jihar New York
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG