Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hare haren Rasha A Syria Ya Halaka Farar Hula Akalla 10.


Smoke rises over Golan Heights as it's seen from Deraa area, Syria July 6, 2018.
Smoke rises over Golan Heights as it's seen from Deraa area, Syria July 6, 2018.

Dumbin fararen hular kasar Syria dauke da farar tuta sun yi tattaki sannu-a-hankali, zuwa kan iyakar Isra’ila da ke gefen yankin “Golan Heights” a wani yunkuri na neman kariya daga hare-haren Rasha da Syria.


Dakarun Syria sun kaddamar da samame, a wani kokari da suke yi na kwato sauran yankun karshe da ke hannun ‘yan tawaye a kudu maso yammacin kasar, inda kusan mutane dubu 160 suka makale a tsakiya.


A jiya Talata, harin sama da aka kai akan tungar ‘yan tawayen da ke Lardin Daraa, ya kashe mutum 10, bayan da wani makami ya dira akan wata makaranta da ake amfani da ita a matsayin mafaka.


Amma kungiyar kare hakkin dan adam ta Syrian Observatory for Human Rights, ta ce, mutum 14 ne suka mutu inda ta da dora alhakin harin akan Rasha.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG