Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Komai na Tafiya Daidai a Taron da Akeyi tsakanin Trump da Putin


Gabanin taron, shugaba Donald Trump ya ce dangantakar dake tsakanin Amurka da Rasha ta fuskanci koma baya a cikin shekarun da suka gabata.

Shugaban Amurka Donald Trump yace taron kolin nan da aka dade ana jira a tsakaninsa da shugaban Rasha Vladimir Putin a Helsinki dake kasar Finland “yana tafiya da kyau, yadda ake so.” Trump ya bayyana haka ne bayan sun share sa’oi biyu suna ganawar ido-da-ido, su kadai, shi da shugaban na Rasha.

Kafin ya je ganawar ido-da-idon da ta yau Litinin, Trump ya ce dangantaka tsakanin kasashen biyu ta sami rauni a ‘yan shekarun da suka gabata amma ya ce “ina gani a karshe zamu sami kyakkyawar dangantaka.

Yayinda aka raka ‘yan jarida waje, shugabannin kasashen biyu sun yi watsi da tambayoyin da ‘yan jaridar suka yi ta yi masu akan katsalandan Rasha a zaben shugaban Amurka na shekarar 2016.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG