Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Farashin Raguna Yayi Tashin Gwauran Zabi


Yayin da sallar layya ke karatowa farashin raguna ya tashi a wata kasuwar dabbobi dake cikin birnin Ibadan fadar gwamnatin jihar Oyo.

Kasuwar dabbobi dake unguwar Arisekola cikin garin Ibadan inda fatake daga arewacin Najeriya da Niger da Mali ke kai raguna.

Wanda ya kawo raguna daga Sokoto yace kasuwar bana sai dai ace an godewa Allah domin ta sha banban da shekarun baya. Rashin kudi a gari ya haddasa masu wani bala'i. Ragun da bara an sayar dashi dubu talatin a wannan shekarar ya kai dubu talatin da biyar.

Wani da ya fito daga kasar Niger kan iyaka da Mali yace kasuwa na tafiya daidai gwargwado. Rashin biyan ma'aikata a kan kari shi ya haddasa tsadar raguna inji shi. Yayin da mutane suka fito da yawa raguna kuma sun soma karanci. Akwai wanda ya kawo karuna tirela daya daga wani sashen Niger.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:14 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG