Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fashewar Motar Iskar Gas A Kenya Ya Kashe Mutane Uku, Da Jikata 270


Wata Mummunar gobara a Nairobi, Kenya
Wata Mummunar gobara a Nairobi, Kenya

Wata mota da ke dauke da iskar gas ta fashe tare da tayar da gobara da ta kona gidaje da dakunan ajiya a babban birnin kasar Kenya da sanyin safiyar Juma'a, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane akalla uku tare da jikkata sama da 270, inda ake sa ran adadin wadanda suka mutu zai karu.

WASHINGTON, D. C. - Ana sa ran yawancin mazauna unguwar da lamarin ya faru na cikin gidajensu lokacin da gobarar ta isa gidajensu da daddare a kusa da Mradi da ke unguwar Nairobi a Embakasi, in ji kakakin gwamnati Isaac Mwaura.

Masu kashe wuta a Kenya
Masu kashe wuta a Kenya

Fashewar babbar motar ta tayar da gagarumar wuta wadda ya yi sanadin kuma ta da gobarar da ta kona Oriental Godown, wani wurin ajiyar kaya da ke hada-hadar tufafi da masaku, in ji Mwaura.

Mwaura ya kara da cewa gobarar ta tashi da misalin karfe 11:30 na daren Alhamis, inda ta lalata wasu motoci da wuraren kasuwanci da dama.

A wurin da lamarin ya faru bayan gari ya waye, an gano cewa gidaje da shaguna da dama ne suka kone.

Gobara a Nairobi, Kenya
Gobara a Nairobi, Kenya

Gangar motar da ake kyautata zaton ya tayar da fashewar yana kwance a gefenta.

Gobarar ya yi sanadin karyewar rufin wata bene mai hawa huɗu da ke da nisan mita 200 daga wurin da fashewar ta faru.

A yanzu haka, dimbin wayoyin lantarki na kwance a ƙasa. Babu wani abu da ya yi saura a cikin rumbun ajiyar kayan da ya kone sai gangar manyan motoci da dama.

Ana kokarin fitar da mutane a wata gobara a Nairobi, Kenya
Ana kokarin fitar da mutane a wata gobara a Nairobi, Kenya

'Yan sanda da kungiyar agaji ta Red Cross ta Kenya sun bayar da rahoton mutuwar mutane uku. Yawan mutanen na iya karuwa bayan gari ya waye, in ji Wesley Kimeto, Shugaban 'Yan Sandan Embakasi.

Gwamnati da kungiyar agaji ta Red Cross sun ce an kai mutane 271 zuwa asibitoci da dama da suka samu raunuka.

Ana kokarin kashe wuta a Kenya
Ana kokarin kashe wuta a Kenya

Ratar kamfanin masana'antu da gidaje ya janyo ce-ce-kuce game da bin ka’ida wurin aiwatar da tsare-tsaren birni. Ana zargin jami'an gwamnatin karamar hukumar da karbar na goro don yin watsi da ka'idojin gine-gine.

-AP

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG