Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

FBI Tace Maharin Nan Da Ya Kashe Mutane Bakwai A Amurka Shi Kadai Ya Aikata


Ana Karrama wadanda harin ya rutsa da su

Hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka wato FBI ta ce dan bindigar nan da ya kashe mutane bakwai ya kuma raunata mutane 22 a garin Odessa a ranar Asabar, shi kadai ya aikata kuma ta yuwu bashi da alaka da wata kungiyar ‘yan ta’adda ta gida ko ta waje.

Dan bindigar ya kwace wata babbar motar raba wasiku kuma ya bude wuta akan wasu motoci yayin da yake shara gudu akan wata babbar hanya kafin wani dan sanda ya kashe shi.

Sai dai a cikin wadanda suka mutu har da wani matashi. ‘Yan sanda uku suna cikin wanda suka ji raunuka. Wata yarinya 'yar watannin goma 17 tana cikin wadanda abun ya rutsa da su, da ta rasa hakoranta da dama kuma ya haddasa ramuka a harshenta da kuma lebenta.

Shugaban ‘yan sanda Odessa, Michael Gerke, ya fada jiya lahadi cewa, zuwa lokacin ba su da takamaimiyar amsa kan abin da ya sa shi ko dalilinsa na aikata hakan. Amma suna tunanin cewa shi kadai ya aika wannan mummunan abu.

Gerke ya ki ya bayyana sunan dan bindiga a lokacin da yake ganawa da manema labarai a jiya Lahadi, ya ce baya son ya sa dan bindigar ya zama wani sananne.

Facebook Forum

Ramaphosa Ya Kai Ziyara Najeriya

Lokacinda Ramaphosa Ya Isa Abuja
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:37 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Ana ci gaba da muhawara a kan ko daga wane yanki na Najeriya yakamata shugaban kasar na gaba ya fito

Karin bayani akan Bidiyo

Zabarmawa, Zabuwa, Ghana

Yadda Aka Gudanar Da Wasan Zabuwa A Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:14 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Sabbin kotunan soji a Maiduguri za su yi shari’a ga kanana da manyan sojoji

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG