Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

FIFA Ta Kaddamar Da Bincike Kan Rikicin Da Ya Barke A Wasan Brazil Da Argentina A Maracana


Ana tuhumar Brazil da laifin gazawa da samar da cikakken tsaro a wasan da ta tsara.

Hukumar kwallon kafa ta FIFA ta fara binciken Brazil da Argentina kan abin da ya haifar da wata riga da ta auku a wasan da kasashen biyu suka yi a Maracana.

Rigimar a cewar Kamfanin Dillancin Labarai na AP ta sa an dakatar da wasan na neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya da za a yi a 2026.

Ana tuhumar hukumar kwallon kafar Argentina da laifin haifar da hatsaniya a cikin ‘yan kallo da kuma jinkirin da aka samu wjen gfara wasan.

A ranar Talata Argentina da Brazil suka fafata inda Argentina ta doke Brazil a gidanta da ci 1-0 a Rio de Janeiro.

It kuma Brazil ana tuhumarta da laifin gazawa da samar da cikakken tsaro a wasan da ta tsara.

Fada dai ya barke a tsakanin magoya baya jim kadan bayan da aka kammala taken kasashen biyu.

Hakan ya sa ala tilas aka sa ‘yan wasa suka koma dakin saka kaya, ba a kuma fara wasan ba sai bayan minti 27.

Dandalin Mu Tattauna

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG