Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

FILATO: ‘Yan Bindiga Sun Hallaka Basaraken Gargajiyan Garin Nyalum Da Wadansu Mutane 2


Wasu da aka kashe
Wasu da aka kashe

‘Yan bindiga sun hallaka mutane uku a garin Nyalum dake karamar hukumar Wase a Jahar Filato, ciki har da basaraken gargajiyan yankin

A daren jiya Litinin ne ‘yan bindiga dauke da muggan makamai suka abka wa garin na Nyalum suka hallaka mutane uku suka yi garkuwa da wasu mata suka kuma jikkata wasu mutanen.

Garin Nyalum dake karamar hukumar Wase a Jahar Filato
Garin Nyalum dake karamar hukumar Wase a Jahar Filato

Wani mazaunin kauyen da ya bukaci in sakaya sunansa, saboda tsaro yace ‘yan bindiga sun mai da kauyukan nasu fagen dagar yaki.

Yan bindiga
Yan bindiga

A hirar shi da Muryar Amurka, kakakin rundunar ‘yan sandan Jahar Filato, DSP Alfred Alabo ya tabbatar da aukuwar harin, sai dai yace har lokacin da Muryar Amurka ke magana da shi bai sami cikakken bayani daga DPO'n yankin ba.

Dazukan dake kananan hukumomin Wase da Kanam dake makwabtaka da juna, sun kasance tamkar mafakan ‘yan ta’adda, don haka al’ummar kauyukan ke neman dauki.

Saurare rahoton a sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:42 0:00

XS
SM
MD
LG