Shugaban kwamitin CNDP mai alhakin warware rigingimun siyasa wato Firai Ministan Jamhuriyar Nijer Birgi Rafini ya yi karin haske game da abubuwan da suka kawo rashin jituwa a zaman kwamitin na karshen makon jiya bayan da hukumar zabe ta zo da wani sabon jaddawalin zaben kasar, koda ya ke ‘yan hamayya na cewa da gangan aka dage zaben saboda wata manufa.
A taron manema labaran da ya kira a washe garin zaman da ya hada wakilan jam’iyyu masu mulki da ‘yan baruwanmu, shugaban hukumar zabe Firai Minista Birgi Rafini mai mukamin shugaban kwamitin CNDP ya bayyana cewa, an dan fuskanci tayar da jijiyoyin wuya daga wajen wasu mahalarta wannan taro, bayan da hukumar zabe ta sanar cewa ba za a iya gudanar da zaben kananan hukumomi a ranar 1 ga watan Nuwamba ba.
‘Yan adawa wadanda suka shafe sama da shekara daya suna kauracewa zaman kwamitin CNDP na kallon matakin daga wannan zabe a matsayin wata makarkasiya da nufin biya wa gwamnati mai ci damar cimma burin da ta sa gaba. Shugaban kawancen jam’iyyun hamayya na Front Patriotique Alhaji Ibrahim Yacouba ya ce, shekara tara kenan ba a gudanar da zaben kananan hukumomi ba, ya kamata a bai wa wadannan kananan hukumomin dama.
Ka-ce-na-ce a tsakanin ‘yan adawa da masu mulki a wannan lokaci da shirye-shiryen zabe ya kankama wata matsala ce da ka iya rage wa zaben kasar ta Nijer armashi saboda haka Birgi Rafini ke sake nanata kiran cewa ya kamata ‘yan adawa su fito a hada kai da su a gudanar da shirye-shiryen zabe lafiya.
Saurari karin bayani cikin sauti.
Facebook Forum