Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Firai Ministan Australia Ya ce Amurka Za Ta Karbi 'Yan Gudun Hijra


Firai Ministan Australia Minister Malcolm Turnbull
Firai Ministan Australia Minister Malcolm Turnbull

Firai Ministan Australia Malcolm Turnbull ya ce Amurka ta himmatu saboda haka mutunta yarjejeniyar sake tsugunar da wasu masu neman mafakar siyasa.

Wadannan mutanen dai an tsugunar dasu a sansanin da ke tsibirin Pacific, duk kuwa da dakatar da amsar 'yan gudun hijira da Amurka tayi.

Yarjejeniyar, wadda aka cimma a zamanin tsohon Shugaba Barack Obama, ta shafi 'yan gudun hijira wajen 1,200 wadanda aka tare su yayin da su ke kokarin kaiwa ga Australia aka kai su sansanonin da ke Papua New Guinea da Nauru.

Mai magana da yawun Fadar White House Sean Spicer ya fadi ranar Talata cewa za’a yi binciken kwakwaf ma duk bakin hauren.

Donald Trump ya fara amfani da wannan kalami na "binciken kwakwaf" yayin yakin neman zabensa don bayyana tsananta bincike ga duk wanda zai shiga Amurka.

XS
SM
MD
LG