Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Firai Ministan kasar Rasha ya yi barazanar ganin abin kunya kan kudurin kasar Siriya


Jakaden kasar Siriya a Majalisar dinkin duniyas Bashar Ja'afari

Ministan harkokin kasashen ketare na kasar Rasha Segev Lavrov ya kushewa daftarin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya kan tashin hankalin da ake yi kasar Siriya

Ministan harkokin kasashen ketare na kasar Rasha Segev Lavrov ya kushewa kalaman daftarin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya kan tashin hankalin da ake yi kasar Siriya da cewa, za a yi abin kunya idan aka kada kuri’a a kai.

Lavrov yace Rasha tana so a yi gyare gyare biyu a daftarin. Bisa ga cewarshi, kamata ya yi matakin da za a dauka ya zama bai daya kan dakarun dake goyon bayan gwamnati da kuma masu adawa domin kada ya zama tamkar ana goyon bayan wani bangare daya a yakin. Ya kuma ce ya kamata daftari ya toshe duk wata damar sab akin kasashen ketare a rikicin.

Ministan harkokin kasashen ketare na kasar Rashan ya bayyana haka ne a tashar jirgin sama ta birnin Moscow kafin ya tashi zuwa jamus yau asabar inda ya yi jawabi ga wani taron kwararrun harkokin tsaro a Munich. Ana kyautata zaton kwamitin sulhun zai kada kuria’a a birnin New York kan kudurin yau asabar.

Masu fafatukar kare hakkokin bil’adama sun ce dakarun kasar Siriya sun kashe a kalla mutane maitan da goma sha bakwai a birnin Homs a wani tashin hankalin da ya barke jiya asabar, yayinda Majalisar Dinkin Duniya take shirin kada kuri’a kan kudurin da zai kawo karshen zubar da jini a kasar.

Kungiyar sa ido kan kare hakin bil’adama ta kasar Siriya ta bayyana jiya jumma’a cewa an kuma jiwa daruruwan mutane raunuka yayinda aka lalata gine gine. An bude wutar ne akasari a unguwar Khalidiya dake birbin Homs inda ake kazamin nuna kin jinin gwamnati. Birnin dake yammacin Siriya kusa da kan iyakar kasar Lebanon, ya kasance daya daga cikin biranen da aka fara zanga zangar kin jinin gwamnati kusan watanni goma sha daya da suka shige.

XS
SM
MD
LG