Accessibility links

Rasha Tace Bata Amince Daftarin Kuduri Kan Syria A Majalisar Dinkin Duniya Ba.

  • Aliyu Imam

Wakilan kwamitin masu aikin sa ido a Syria, lokacind a suka ziyarci yankin Da'raa.

Rasha ta bayyana rashin amincewarta kan daftarin kudurin hadin guiwa da turai d a kasashen larabawa suka wallafa aka rabawa wakilan kwamitin sulhu a jiya jumma’a.

Rasha ta bayyana rashin amincewarta kan daftarin kudurin hadin guiwa da turai da kuma kasashen larabawa suka wallafa, aka rabawa wakilan kwamitin sulhu ranar jumma’a. Duk da haka Moscow tace a shirye take a yi shawarwari.

Jakadan Rasha a Majalisar Dinkin Duniya Vitaly Churkin, yace daftarin baiyi la’akari da sassa da Rasha ko kusa ba zata amince dasu ba, kamar takunkumin hana sayarwa Syria makamai.

Daftarin ya goyi bayan kduurind a kungiyar hada kan kasashen larabawa ta zartasa wadda ya nemi shugaba Assad ya mika iko ga mataimakinsa a kafa gwamnatin hada kan kasa, san a shirya yin zabe.

Ana sa ran ranar talata mai zuwa babban sakatern kungiyar kasashen larabawan Nabil AlAraby, da PM Qatar zasu yi bayani ga wakilan kwamitin sulhu kan ayyukan wakilan ayyukan sa ido da kungiyar ta tura Syria wadda suka yi aiki na tsawon wata daya a Syria kuma suka fuskanci matsaloli yayin wan nan aiki.

Haka kuma ana ji cikin makon mai zuwa ne kungkyar zata gabatar wa kwamitin sulhu wan nan kuduri data zartas a hukumance, daga nan ne ake sa ran kwamitin sulhun zai kada kuri’a akai ba da jumawa ba bayan haka.

Ahalinda ake ciki kuma tarzoma sai kar a tsanani take a Syrian a jiya jumma’a , har kaa bada rahoton an kashe akalla mutane 70 a baya bayan nan.

XS
SM
MD
LG