Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Firaministan Chadi Ya Mika Takardar Murabus Ga Sabon Zababben Shugaban Mulkin Soji


Success Masra
Success Masra

"Kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada, a yau na gabatar da... murabus di na da na gwamnatin rikon kwarya, wanda bai da alaka da karshen zaben shugaban kasa na ranar 6 ga Mayu," in ji Masra a ranar Laraba a shafin X.

A yau, Laraba Firai Ministan Chadi Success Masra yace ya mika takardar murabus dinsa, makonni biyu bayan kayen da ya sha a hannun shugaban mulkin sojan kasar Mahamat Idriss Deby Itno a zaben shugaban kasa.

Ya kara da cewa matakin ya kuma yi daidai da kundin tsarin mulkin kasar.

An Ayyana Deby, mai shekaru 40 ne a matsayin shugaban rikon kwarya a watan Afrilun 2021 ta hannun wasu sojoji 15.

Wannan dai ya zo ne bayan da mahaifinsa, shugaban kasa Idriss Deby Itno, da 'yan tawaye suka harbe shi, bayan shafe shekaru 30 yana mulki.

Kamfanin dillancin labaran Faransa AFP ya ce ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar 6 ga watan Mayu da kashi 61 na kuri'un da aka kada.

Shugaban Chadi Mahamat Idriss Deby / AFP.
Shugaban Chadi Mahamat Idriss Deby / AFP.

Shi ma Masra mai shekaru 40, wada ya taba zama abokin hamayyar Deby kafin ya zama Firai Minista watanni hudu da suka gabata, inda ya samu kashi 18.5 na kuri'un da aka kada amma ya ki amincewa da sakamakon.

Nasarar Deby ta tsawaita wa'adin mulkin danginsa da suka yi kaka-gida a kan mulki tun lokacin da mahaifin Deby ya karbi mulki a wani juyin mulki a farkon shekarun 1990.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG