Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Firayim Ministan Kasar Mali Da Mambobinsa Sunyi Ritaya


Firayim Ministan kasar Mali Soumeylou Boubeye Maiga da dukan mambobin gwamnatinsa sun yi murabus a jiya Alhamis.

Wata sanarwa daga ofishin shugaban kasar Ibrahim Boubacar Keita ta ce: "Shugaban kasa ya amince da murabus din na firaministan kasar da na mambobin gwamnatin sa."

Wannan mataki ya zo ne bayan tashe tashen hankula a yankin tsakiyar kasar, ciki har da kisan gilla a watan jiya na Fulani 160, wanda ake zargin mafarauta na Dogon ne suka aikata.

Majalisar Dinkin Duniya ta fitar rahoton cewa, a cikin shekarar da ta wuce, fada tsakanin Fulani da al’umar Dogon ya janyo mutuwar mata da yara da maza har guda 600.

Makonni biyu da suka wuce an yi zanga-zanga a garin Bamako, babban birnin kasar, don nuna rashin amincewa da rashin ikon gwamnati na hana aukuwar tashe tashen hankula.

Facebook Forum

Wani Sirri Da Tsohon Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou Ya Fadawa ‘Sarki Sanusi II’
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:23 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

An Kai Wa Ofisoshin Kungiyar Ba Da Agaji Hari A Arewa Maso Gabashin Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:02 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG