Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Nijar Za Ta Fara Nada Shugabannin Jami’o’i Maimakon Zabensu


NIGER: SHUGABA MUHAMMADOU ISSOUFOU
NIGER: SHUGABA MUHAMMADOU ISSOUFOU

Majalisar Dokokin Jamhuriyar Nijer ta amincewa wata dokar dake baiwa gwamnati hurumin nada shuwagabanin jami’o’i a maimakon a zabe su.

Matakin da ake ganin zai taimaka a magance matsalolin dake dabaibaye sha’anin karatu a jami’o’in kasar sai dai kungiyar malamai na cewa ba za ta sabu ba.

Da kuri’u 135 daga cikin 171 ne Majalisar ta yi na’am da wannan kudirin doka mai kunshe da wasu mahimman sauye-sauye da suka shafi tsarin tafiyar da harakokin jami’o’in gwamnatin Nijer cikin su har da batun maye gurbin zaben shuwagabanin jami’oi da wani tsarin na daban wanda a karkashinsa hukumomi za su sami hurumin nada irin wadanan jami’ai, mataimakin shugaban Majalisar Dokokin kasa IRO SANI ya bayyana dalilansu na amincewa bukatar gwamnatin ta Nijer.

Kungiyar malaman jami’o’i ta SNECS wacce ta shafe watanni ta na yajin aiki akan batun zabe ko nadin shuwagabanin jami’oi ta yi watsi da wannan mataki da take ganinsa a matsayin wanda ya sabawa tafarkin dimokradiya. Madame FATIMA MAYAKI ita ce mataimakiyar sakataren wannan kungiya.

To amma Majalisar Dokokin na gargadin malaman jami’oi da su yi karatun ta nutsu don kaucewa aikata dukkan wani abin da ka iya dabaibaye al’amuran ilimi a wannan kasa.

Ranar Asabar ne ministan ilimi mai zurfi Yahouza Sadissou ke hallara zauren Majalisa domin yiwa wakilan al’uma bayani akan matsalolin dake yiwa sha’anin karatu tarnaki a daukacin jami’o’in gwamnatin Nijer.

Domin cikakken bayani saurari rahotan Sule Muminu Barma.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG