A wani jawabi yau Alhamis a kafar talabijin, Davutoglu ya ce ‘yan kungiyar awaren PKK ta kurdawa ne su ka kai harin “tare da wani mutum da ya silale zuwa cikin Turkiyya daga Siriyya.
Davutaglu ya ce dan Syrian, da dan kungiyar ‘yan tawayen YPG ne suka shirya kai harin. Amma kasar Turkiyya ta dauki duka kungiyoyin YPG da PKK a matsayin na ‘yan ta’adda.
Saleh Muslim, shine shugaban kungiyar ta kurdawa, ya musanta zargin da Turkiyya ke yi masu, ya ce kungiyar ba ta da wata alaka da harin bamabaman.
Harin da aka kai jiya Laraba, an auna wata tawagar motocin sojan kasar ne a babban birnin Turkiyya, inda ba ya da nisa sosai da helkwatocin ‘yan majalisa da na rundunar sojan kasar.