Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Firayi-Ministan Birtaniya Zai Ziyarci Brussels Bayan Fitar Ingila Daga Tarayyar Turai


David Cameron, Firayi-Ministan Birtaniya
David Cameron, Firayi-Ministan Birtaniya

Yau Talata wata rana ce mai cike da takaici yayin da Firai ministan Birtaniya David Cameron zai yi tattaki zuwa Brussels domin ganawa da shugabannin kungiyar tarayyar Turai ta EU.

Ziyayar ta sa ita ce ta farko tun bayan da aka jefa kuri’ar raba gardama kan ficewar kasar daga EU, kuma zai fuskanci tambayoyi kan yadda da kuma yaushe Birtaniyar ta shirya ficewa daga kungiyar.

“Ina so Birtaniya ta fayyace komai kan matsayarta, ba wai a bari sai yau, ko gobe da misalin karfe tara na safe ba, amma dai nan ba da jimawa ba.” Inji kwamishinan kungiyar ta EU, Jean Claude Juncker, yayin wani taron gaggawa da aka yi a yau a zauren majalisar.

Su dai shugabannin kasar ta Birtaniya ba sa nuna wata alama da ke nuna cewa suna hanzarin shirin ficewa daga kungiyar, koda ya ke, Firai minister David Cameron mai barin gado, ya ce ba huruminsa ba ne, aiki ne na wanda zai gaje shi.

Inda za a aiwatar da sashin nan mai lamba 50 da aka amince da shi a taron Lisbon, wanda zai share hanyar ficewar kasar daga kungiyar. A ranar Alhamis, jam’iyar Kwanzavative ta Cameron za ta fara shirin neman wanda zai maye gurbinsa, inda ake sa ran za su zabi wani nan da ranar biyu ga watan Satumba.

Sai dai Faransa da sauran mambobin kungiyar ta EU, suna ganin Birtaniyar na jan kafa wajen ficewar, wanda hakan su ke ganin ya kara haifar da illoli ga tattalin arzikin yankin wanda tuni ya ke fuskantar barazana.

XS
SM
MD
LG