Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fitattun Sojojin Amurka Sun Kashe Shugaban IS Abu Ibrahim al-Hashimi al-Qurayshi


Fitattun sojojin Amurka sun kashe shugaban kungiyar IS, a wani samame da suka kai cikin dare a lardin Idlib da ke arewa maso yammacin Syria, in ji shugaban kasar Joe Biden.

An kai harin ne kan Abu Ibrahim al-Hashimi al-Qurayshi, wanda ya karbi ragamar shugabancin kungiyar a ranar 31 ga Oktoba, 2019, kwanaki kadan bayan mutuwar shugaba Abu Bakr al-Baghdadi a wani farmaki da Amurka ta kai a yankin.

Wannan farmakin ya zo ne a daidai lokacin da kungiyar IS ke kokarin sake bullowa, tare da kai wasu hare-hare a yankin, ciki har da harin kwanaki 10 a karshen watan da ya gabata na kwace wani gidan yari.

Dakarun Amurka na musamman sun sauka ne a cikin jirage masu saukar ungulu tare da kai farmaki a wani gida a wani yanki da ke hannun ‘yan tawaye a Syria, inda suka shafe sa’o’i biyu suna artabu da ‘yan bindiga, kamar yadda shaidu suka bayyana.
Mazauna yankin sun bayyana ci gaba da harbe-harbe da fashe-fashe da aka yi a garin na Atmeh da ke kusa da kan iyakar Turkiyya, yankin da ke da sansanonin 'yan gudun hijira daga yakin basasar Siriya. Masu bada bayani na farko sun ce an kashe akalla mutane 13 da suka hada da yara shida da mata hudu.

Shugaban Azman

Dalilin Da Yasa Muka Dakatar Da Tafiya Yajin Aikin Sufurin Jiragen Sama a Najeriya - Shugaban Azman
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:17 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Sojojin Najeriya sun samu nasarar kwace bindigogi sama da 500

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Shugaban NDLEA a Najeriya, Janar Buba Marwa

Dalilin Da Ya Sa Muke Bin Diddigin Dukiyar DCP Abba Kyari - Buba Marwa
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Yadda Rikicin ‘Yan Aware A Yankin Kamaru Ya Shafi Wasu Al’ummoni A Najeriya

Yadda Rikicin ‘Yan Aware A Yankin Kamaru Ya Shafi Wasu Al’ummoni A Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:19 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Gwamna Matawalle

Dalilan Da Suka Sa Muka Sayi Motoci Ga Sarakuna A Zamfara - Gwamna Matawalle
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:35 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG