Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fiye da mutane dudu daya da dari ne ambaliyar ruwa ta kashe a arewa maso yammacin Pakistan


Fiye da mutane dudu daya da dari ne ambaliyar ruwa ta kashe a arewa maso yammacin Pakistan

Ma'aikatan ceto a arewa maso yammacin Pakistan suna can suna kokarin cewa mutanen da ambaliyar ruwa ta rutsa dasu. Fiye da mutane dudu daya da dari tara ne ambaliyar ta kashe.

Ma’aikatan aiyukan ceto a arewa maso yammacin kasar Pakistan suna can suna fafitukar kaiwa ga dubban kauyawa da mumunar ambaliyar ruwa ta rutsa dasu, kuma an baiyana cewa a jiya lahadi fiye da mutane duba daya da dari daya ne suka mutu. Jami’an yankin sunce ruwan sama da aka yi ta tapkawa kamar da bakin kwarya har na tsawon mako guda ne suka hadasa a,baliyar ruwa. Ambaliyar kuma ta fi yiwa lardin Khyber Pakhtunkhwa barna. Jami’an sun yi kashedin cewa za’a yi ta samu karuwar wadanda suka mutu, sun kuma baiyana tsoron cewa za’a samu bular anobar gudawa da kwalera. A sanarwar data gabatar a jiya lahadi, sakatariyar harkokin wajen Amirka Hillary Clinton tace Amirka tana jinjinawa yan Pakistan kuma ofishin jakadancin Amirka a birnin Islamabd zai bada dala miliyan goma na taimakon jin kai. Muna da karin bayani bayan labarum duniya.

XS
SM
MD
LG