Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Amurka Barack Obama zai tattauna da shugabannin matasan nahiyar Africa


Shugaban Amurka Barack Obama zai tattauna da shugabannin matasan nahiyar Africa

Shugaban Amurka Barack Obama zai tattauna da shugabannin matasan nahiyar Afrika na tsawon sa’a daya da rabi yau Talata a fadar shugaban kasa ta White House.

Shugaban Amurka Barack Obama zai tattauna da shugabannin matasan nahiyar Afrika na tsawon sa’a daya da rabi yau Talata a fadar White House, su kuma matasan zasu tofa albarkacin bakinsu ta hanyar tambayoyi kan abinda ya daure masu kai. Za a kuma nuna tattaunawar kai tsaye ta kafar intanet. Shugaban Amurkan zai yi wannan tattaunawar ne da shugabannin matasan nahiyar Afrika ne a daidai lokacin da kashen nahiyar Afrika goma sha bakwai ke bukukuwan cika shekaru hamsin da samun ‘yancin kansu, don haka babu ko guda daya daga cikin shugabannin Afrika dake halartar wannan zaman taron na yau a nan Amurka. Daga cikin shugabannin matasan kasashen Afrika da aka gayyata domin wannan tattaunawar da shugaba Barack Obama, akwai kwararru masana a sassa dabam-dabam na halin zaman rayuwar al’umma, akwai kuma ‘yan kasuwa, da ‘yan jarida da shugabannin mata da kuma shehunan malamai.

White House
White House

Shugabannin matasan kasashen Afrika zasu kai ziyarar gani da ido ma’aikatar harkokin wajen Amurka da wadansu muhimman wuraren tarihi inda zasu maida hankali da tambayoyi a fannin ilimi da kiwon lafiya da harkokin cinikayya.

XS
SM
MD
LG