Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fiye Da 'Yan Gudun Hijiran Afghanistan Miliyan Daya Ne Suka Koma Gida Da Kansu


Gwamnatin kasar Afghanistan ta bayyana a yau Litinin cewa fiye da yan gudun hijira Miliyan daya ne suka komo gida dakansu daga Pakistan da Iran a shekarar 2016 wanda ya nuna adadi mafi yawa da aka samu na wadanda suka dawo a cikin shekaru 14.

Ministan Baki da kuma masu dawo da kansu Sayed Hussain Alimi Balkhi ya fadawa Yan majalisun kasar cewa wadanda suka dawo da kawunannasu daga makwabtan kasar sun hada da Iyalan da akayi musu rijista da kuma wadanda ba’ayimusuba.

Sannan ya kara da cewa, akwai Yan Kasar Afghanistan kimanin 551,000 da suka gudu daga gidajen su a wannan shekarar sakamakon fadace fadace da kuma rashin zaman lafiya. Wanda ya kara yawan adadin wadanda ke zaune a sansanin yan gudun hijira na cikin gida a Afghanistanzuwa Milliyan 1.3 .

MDD ta yi gargadin cewa yanayin rayuwar al’umma ya kara tabarbarewa sakamakon karuwar yawan mutanen da basu da matsuguni a sansanonin, Tabarbarewar da ta afkju ne sakamakon kwararowar Yan gudun hijira kimanin 600,000 wadan da suka dawo kuma ba’a hukunce ba daga Afghanistan.

XS
SM
MD
LG