Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Floyd: Yadda Aka Ci Gaba Da Zanga Zanga a Sassan Duniya


Dubban masu zanga zangar adawa da nuna wariyar launin fata a sassan duniya, sun bazama a titunan biranen Roma, Berlin, London da kuma Paris.

Yayin da wasu masu zanga zangar sun harzaka ne sanadiyyar mutuwar George Floyd, ba’amurken nan dan asalin Afirka da ya mutu bayan da wani dan sanda ya danne wuyansa a birnin Minneapolis, wasu a kasashen turai sun yi boren ne domin an sosa musu inda ke musu kaikayi – wato kan yadda ake fuskantar irin wannan matsala a nahiyar ta turai.

A birnin Roma, dubban masu zanga zangar sanye da ababen rufe fuska, sun dunguma a wani fitaccen dandali a jiya Lahadi, wanda wannan shi ne karon farko da aka fara gudanar da zanga zangar adawa da wariyar launin fata a birnin.

A London ma, dubban masu zanga zangar ne suka bazama a tituna wasu kuma a wajen ofishin jakadancin Amurka, duk da cewa jagororin gangamin sun ce muradinsu shi ne su yi yaki da matsalar nuna wariyar launin fata a Birtaniya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG