Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

GABAS TA TSAKIYA: Amurka Zata Sake Lale A Tsarin Tallafawa Tsirarru


Mataimakin shugaban Amurka Mike Pence
Mataimakin shugaban Amurka Mike Pence

Mataiamakin shugaban kasar Amurka Mike Pence yace ma’aikatar harkokin wajen Amurka ba zata ci gaba da bada kudi a shirin Majalisar Dinkin Duniya da bashi da tasiri ba, na tallafawa mabiya wadansu addinai tsirarru a kasashen Gabas ta tsakiya, a maimakon haka za a rika tallafa masu kai tsaye karkashin shirin cibiyar bunkasa kasashen duniya na Amurka.

Pence ya sanar da haka ne jiya da dare a wajen wata walima da wata kungiya dake hankoron wayar da kan al’umma kan halin da kirista suke ciki a gabas ta tsakiya.

Mataimakin shugaban kasar yace Majalisar Dinkin Duniya ta gaza taimakawa tsirarru mabiya wadansu addinai, ta kyalesu suna shan wahala ba gaira ba dalili.

Pence bai ambaci kasashen da abin ya shafa ba, ko lokacin da za a yi wannan canjin, ko kuma yawan kudin da za a ware daga gudummuwar da Amurka ke ba Majalisar Dinkin Duniya ba.

Yace ana kuntatawa addinin kirista a kasashen da addinin ya fara samun tushe, yana ambaton musamman kasashen Iraq da Syria da Misira da kuma Lebanon.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG