Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gada Daya Tilo da Ta Hada Biranen Yaunde da Douala A Kamaru Ta Rushe


 Gada daya tilo da ta hada biranen Yaunde da Douala ta rushe
Gada daya tilo da ta hada biranen Yaunde da Douala ta rushe

Gadar dake kan hanyar da ta hada birnin Douala birnin kasuwancin kasar Kamaru da birnin Yaunde fadar gwamnatin kasar ta rushe lamarin da ya yanke biranen daga sauran kasar

Wannan hanyar ita ce ta hada biranen musamman wajen harkokin yau da kullum mafi sauri.

Alhaji Bakari shugaban masu manyan motoci na kasar Kamaru yace ya ga wurin kuma ruwa ne kawai yake kwarara. Babu yadda zasu wuce da motocinsu. Yace fiye da awa goma babu motsi ko kadan saboda babu hanya. Lamarin ya sa sun rasa dukiyoyi, kasar kuma tana cikin matsala. Yanzu mai son wucewa sai ya kewaya ta garin Izika, kewayen da yake masifa ne domin ga nisa ga rashin kyawon hanya.

Hanyar ke nan kafin rushewar gadar
Hanyar ke nan kafin rushewar gadar

Malam Bashir da yake kan hanyarsa ta zuwa birnin Yaunde daga Douala yace sun tsinci kansu a kan hanya sun rasa yadda hakan ya faru. Wai wasu ne suka fada masu cewa ruwan sama da aka yi da dare ya haddasa rushewar gadar. Yayi mamakin yadda za'a ce hanya tak ta hada manyan biranen?.

Danladi Muazu dan kungiyar farar hula yayi zargin cewa cin hanci ya sa ana aikin gina hanya ba tare da bin ka'ida ba. A cewarsa yakamata ayi bincen kwakwaf akan lamarin.

Yanzu dai jiragen sama da na kasa ne suke iya zirga zirga tsakanin biranen biyu.

Ga rahoton Garba Lawal da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:25 0:00

XS
SM
MD
LG