Wannan lamarin ya bayyana ne a taron da kungiyar ta gudanar na farko bayan zaben, inda gwamnoni goma sha hudu daga cikin goma sha tara dake kungiyar suka kauracewa taron.
Gwamnonin da suka tura wakilai a maimakon halarta da kashin kansu sun hada da Kano, Borno, Zamfara, Sokoto, Kebbi Kogi, Kwara, Katsina, Benuwe da Plato, yayinda gwamnonin Adamawa Taraba da Yobe suka nemi ahuwa saboda bisa ga cewarwu, suna da uzuri, shi kuwa gwamna Isa Yuguda na jihar Bauchi, cika alkawarin da ya yi ne cewa, ba zai sake halarta taron kungiyar ba sai an bayyanawa jama’a shawarar da kungiya ta yanke dangane da zaben shugaban kungiyar gwamnoni na kasa.
Wakilinmu Isah Lawal Ikara ya halarci taron ya kuma hada mana rahoto.