Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ganawar Sirri Tsakanin Obasanjo Da Secondus Kan Rikicin Cikin Gida Na PDP


Uche Secondus, Shugaban Jam'iyyar PDP

Shugaban jam’iyyar PDP Uche Secondus ya yi ganawar sirri da tsohon shugaban Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo a Abeokuta ta jihar Ogun, a bisa dalilin neman bakin zare warware rikicin cikin gida da ya dabaibaye jam’iyyarsa ta PDP.

Secondus da Obasanjo dai sun shafe sama da sa’a guda suna ganawar sirri da suka kammala da misalin karfe 2 da minti 6 na ranar Alhamis, a birnin Abeokuta kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Majiyoyi sun bayyana cewa Secondus ya yi tattaki zuwa Abeokuta ne don ba da bayanin halin da ya ke ciki da zimmar Obasanjo ya shiga tsakani kuma ya sa baki don sasanta rikicin.

Saidai wata majiyar ta ce tsohon shugaba Obasanjo ya nanata matsayinsa na cewa ya daina yin siyasar, amma kofofinsa a bude suke don ba da shawara.

Tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo (Instagram/ olusegun obasanjo)
Tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo (Instagram/ olusegun obasanjo)

Ana dai ganin cewa ganawa tsakanin Obasanjo da Secondus na zuwa ne bisa rushewar matsayar da aka cimma a wani taro da aka yi a baya a birnin Minna na Jihar Neja.

Rahotanni daga jam’iyyar PDP sun yi nuni da cewa an sami sabani kan shirin warware rikicin cikin gida tsakanin jiga-jigan jam’iyyar adawa ta PDP inda aka yi watsi da wasu matsaya da aka cimma a babban taron kwamitin zartarwata na ranar Talata 10 ga watan Agusta.

Haka kuma majiyoyi daga cikin jam’iyyar sun bayyana cewa duk da an amince a taron na ranar 10 ga watan Agusta cewa ya kamata a gudanar da babban taron jam'iyyar a watan Oktoba, kwamitin gudanarwa na jam’iyyar na kasa karkashin jagorancin shugaban jam’iyyar ta PDP Uche Secondus ya gabatar da dalilan da yasa ba za’a iya yin taron a watan Oktoba ba.

Sai dai wasu rahotanni daga cikin jam’iyyar sun ce wani bangare a cikin jam’iyyar mai hamayya, wanda ke karkashin jagorancin gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas, ya yi watsi da uzurin Uche Secondus, yana mai cewa dabara ce ta zaunawa daram a matsayin shugaban jam’iyyar ta PDP.

Rahotanni dai sun yi nuni da cewa a bisa dalilin sabon rikicin da ke cikin jam'iyyar, akwai yiyuwar a sake yin wani taron kwamitin gudanarwar jam’iyyar wato NEC a watan gobe na Satumba.

Idan ana iya tunawa a cikin makwanni biyu da suka gabata ne rikicin ya sake barkewa tsakanin mambobin jam’iyyar PDP sakamakon zargin da ake yiwa wani tsagi a cikin jam’iyyar da shirin cire Secondus a matsayin shugaban jam’iyyar.

Masu fafutukar na zargin cewa shugaban yana shirin shigar da amintattunsa a matsayin mambobin kwamitin babban taron kasa don tabbatar da sake fitowarsa a matsayin shugaba.

Jita-jitar tsamin dangantaka tsakanin Uche Secondus da gwamna Nyesom Wike dai ta mamaye kafaffen yada labarai, lamarin da ake ganin yana kara kamari.

A wani bangare kuma, ita ma jam'iyyar APC na fama da rikicin cikin gida tsakanin mambobinta da ake ganin shi ya kawo jinkiri a aikin gudanar da zabubbukan shugabanninta daga matakan gundumomin zuwa sama.

XS
SM
MD
LG