Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ganawar Trump Da Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas


Shugaban Amurka Donald Trump da shugaban Falasdinu Mahmoud Abbas sun dau alkawari a jiya Laraba a fadar White House game cimma matakan diflomasiyya wurin kawo zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya.

Shugaba Trump yace yakamata Falasdinawa da Isra’ila su yi aiki tare, ya kuma kara da cewar yana sha’awar ya zama mai shiga Tsakani kuma mai sasantawa da zai tabbatr da zaman lafiya.


Shugaba Trump yace ga baki dayan rauyawarsa ya fahimci sulhu mafi wahala shine sulhu tsakanin Isra’ila da Falasdinu. Yace to bari mu duba ko yalla zamu yi nasara a wannan karo.


Da yake jawabi tare da shugaban Amurka a zauren taron manema labarai na Roosevelt, Abbas ya fada da harshen Larabci cewa yana kyautata zaton bangarorin biyu karkashin jagoranci na karfin hali irin na shugaba Trump, da kuma kwarewarsa wajen shiga tsakani, za a cimma yarjejeniyar zamana lafiya mai tarihi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG