Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump: Ikirarin Hillary Clinton Ihu ne Bayan Hari


Ms. Clinton ta yarda ita ma ta taka rawa wajen faduwarta a zaben shugabancin Amurka da ya gabata.

Shugaban Amurka Donald Trump ya musanta zargin da Abokiyar takararsa a zaben shugabancin kasar Amurka da aka yi a shekarar da ta gabata Hillary Clinton tayi na cewa, shugaban hukumar bincike ta FBI, James Comey na daya daga cikin mutanen da suka yi sanadiyar faduwarta a zaben.

Trump ya rubuta a dandalinsa na Twitter a jiya Talata cewa, a kashin gaskiya ma Comey taimakawa Hillary Clinton yayi da ya bata damar wucewa, sakamakon zarginta da abubuwa marasa kyau da ta aikata. Ya kara da cewa kuma zargin da ake wa Rasha na cewa ta saka hannu a cikin zaben, ihu ne bayan hari na faduwarta zaben.

A jiya Talata ne Clinton ta zargi mutane da dama akan faduwarta a zaben, ciki har da Comey da kuma shafin nan na yanar gizo na Wikileaks, wanda ya buga sakonnin email din da aka sata ta hanyar kutse na kemfe dinta.

Clinton tace “ina kan hanyata ta samun nasara” kafin Wikileaks suka fara fidda sakonnin emails da aka sata na shugaban kamfe dina John Padesta, kuma Comey ya fadawa 'yan majalisar cewa yana binciken sakonnin email din.”

Ta kara da cewa wadannan abubuwan su suka sa masoyanta suka fara kwakkwanto akan ta wanda ya janyo mata asarar Kuri’u, bayanda duk suka tsorata.

Clinton ta ce ita ma ta taka rawa wajen faduwarta a zaben da kuma fahimtar cewar bata gudanar da kamfe mai kayau ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG