Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ganawarmu Ta Yi Kyau Fiye Da Yadda Ake Zato - Trump


Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un da Shugaban Amurka Donald Trump a Singapore inda suka yi taron da ya shiga tarihi
Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un da Shugaban Amurka Donald Trump a Singapore inda suka yi taron da ya shiga tarihi

A cewar shugaban Amurka Donald Trump taron kolin da suka yi da shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un ya yi kyau fiye da yadda aka yi zato har ma zasu rabtaba hannu akan wata yarjejeniya tsakanin kasashen biyu

Shugaba Donald Trump na Amurka yace ganarwasa da takwaran aikin sa na Korea ta Arewa Kim Jong Un tayi kyau sosai, kuma yayi maganar cewa suna da kyakyawar dangantaka a yayinda suka zanta a kasar Singapore yau Talata akan yiwuwar kwashe makamai daga zirin Korea.

Kafin su fara ganawar, shugaba Trump yace daram yake ji, kuma zasu yi tattaunawa mai kyau, yana kuma zaton za’a samu nasarar sosai haka kuma yace yana alfahari da ganin zasu samu kyakyawar dangantaka.

Bayan da suka yi ganawar kimamin mintocin arba’in su biyu kurum in baicin masu yi musu tafinta, Shugaba Trump da shugaba Kim sun gaiyaci yan tawagar wakilansu domin yin shwarwari sosai.

Kafin a fara taron shugaba Trump ya kuma ce zasu samu damar magance babbar matsala.

Shugaba Donald Trump na Amurka yace ganawar tarihi da suka yi yau Talata da takawaran aikinsa na Korea ta Arewa Kim Jong Un tayi kyau fiye da yadda ake zato.

Shugabanin biyu sun fito kafada da kafada bayan cin abincin rana, biyo bayan gawar mintoci arba’in da suka yi, tunda farko su kadai tare da masu yi masu tafinta. Mr Trump yace sun yi kyakyawar ganawar kuma an samu ci gaba sosai. Yace zasu rattaba hannu akan wata yarjejeniya ba tare da bada wani karin haske ba.

Shugabanin biyu dai sun je kasar Singapore yin wannan taro ne da nufin yin shawarwari akan yiwuwar kwashe makamai daga zirin Korea.

Tunda farko baban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guetteres yayi maraba da ganawar da aka yi tsakanin shugabanin Amurka da Korea ta Arewa.

Yace tilas batun samun zaman lafiya da kuma kwashe makamai daga zirin Korea su zama baban burin da aka sa a gaba. Jiya Litinin sakataren na Majalisar Dinkin Duniya yayi wannan furuci a hedikwatar Majalisar a birnin New York

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG