Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ganduje: Jaafar Jaafar Ya Gudu Ingila Tare Da Iyalinsa


Jaafar Jaafar

Bayanai sun yi nuni da cewa, Jaafar ya ce ba zai koma Najeriya ba har sai gwamnati ta bada tabbacin za ta kare lafiyarsa tare da tabbatar da walwalar aikin jarida.

Mawallafin jaridar Daily Nigerian Jaafar Jaafar da ya fitar da wani bidiyo da ke zargin gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje da karbar cin hanci, ya tsere zuwa Ingila.

Jaridar Premium Times wacce ta ce ta yi magana da dan jaridar, ta wallafa a shafinta a ranar Litinin cewa, Jaafar ya gudu ne saboda barazana da ake yi wa rayuwarsa.

Bayanai sun yi nuni da cewa, Jaafar ya ce ba zai koma Najeriya ba har sai gwamnati ta bada tabbacin za ta kare lafiyarsa tare da tabbatar da walwalar aikin jarida.

Rahotanni sun yi nuni da cewa, Jaafar ya bar kasar ne tare da iyalansa.

Lamarin na faruwa ne a daidai lokacin da ake bikin ranar ‘yancin ‘yan jarida ta duniya.

Karin bayani akan: Umar Ganduje, jihar Kano, Nigeria, da Najeriya.

A tsakiyar watan Afrilu Jaafar, ya buya a wani wuri da bai bayyana ba, yana mai cewa jami’an tsaro na kokarin su kama shi inda ya danganta lamarin da batun wannan bidiyo da ya fitar.

Dan jaridar ya bayyana cewa an je har ofis ana nemansa amma ba a same shi ba, lamarin da ya sa shiga halin buya.

“Abin da kake tunanin ka yi don a kawo gyara a cikin al’uma, sai kuma ya zama kai ne ake nema da sharri.” Ja’afar ya fadawa Muryar Amurka a lokacin da yake boye.

Sai dai gwamnatin Kano ta ce ba ta da hannu a zargin da Jaafar ke yi na ana so a kama shi.

Shi dai gwamnan Kano Ganduje ya musanta wannan zargin karbar cin hanci, inda ya ce hotunan bidiyon na bogi ne domin hada su aka yi.

“Kuma abin nan ba kage ba ne, gaskiya ne, kowa ya sani, shi kansa ya sani, mabiyansa sun sani, wadanda suke goyon bayansa sun sani, duk wani jami’i da kika sani ya sani.” Jaafar ya ce.

A shekarar 2018, Jaafar ya fitar da bidiyo da yake zargin Ganduje na karbar cin hancin daloli, wanda gwamnatinsa ta musanta.

Majalisar dokokin jihar ta Kano ta kafa kwamiti don ya binciki sahihancin bidiyon inda har ta gayyaci Jaafar don bayyana a gabanta, ya kuma amsa goron gayyatar.

Kamar yadda rahotanni suka nuna, gwamnati ta hana kwamitin da ci gaba da yin binciken amma an mika batun ga gaban kotu, wacce har yanzu take sauraren karar.

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG