Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Garba Shehu Ne Shugaban Najeriya, Ba Buhari Ko Osinbajo Ba – Bamgbose


Olusegun Bamgbose, Shugaban kungiyar nan mai fafutukar kyakkyawan shugabanci a Najeriya CAGG
Olusegun Bamgbose, Shugaban kungiyar nan mai fafutukar kyakkyawan shugabanci a Najeriya CAGG

Shugaban kungiyar nan mai fafutukar samar da kyakkyawan shugabanci a Najeriya CAGG, Olusegun Bamgbose, ya bayyana masahawarci na musamman ga shugaban Najeriya Muhammadu Buhari akan sha’anin watsa labarai Garba Shehu, tamkar shi ne shugaban kasa, ba Muhammadu Buhari ba.

Olusegun Bamgbose wanda kuma kwararren lauya ne, ya bayyana cewa hatta ofishin mataimakin shugaban kasa ma Garba Shehu ya jingine shi gefe, inda a yanzu shi ne yake gwada ikon tafiyar da aikin shugaban kasa.

Bamgbose ya na maida martani ne akan sanarwowin da Garba Shehu ke fitarwa akai-akai, har ma da wadanda yake ganin kamata yayi ‘yan Najeriya su ji su kai tsaye daga shugaban kasa.

Na baya-bayan nan shi ne sanarwar fadar shugaban kasa da shi Garba Shehun ya fitar, a zaman martani kan matakan da gwamnonin kudancin Najeriya suka dauka.

Gwamnonin na kudu baki dayan su sun gudanar da wani taro a Asaba ta jihar Delta, inda suka tattauna matsalolin tsaro da ke addabar yankin na su, inda kuma suka ba da sanarwar haramta kiwon dabbobi a sarari a jihohin na su.

Gwamnonin Kudancin Najeriya Sun Gudanar Da Taro A Asaba, Jihar Delta
Gwamnonin Kudancin Najeriya Sun Gudanar Da Taro A Asaba, Jihar Delta

Ministan Shari’a Abubakar Malami ya fito ya soki lamirin matakin na gwamnonin, yana mai kwatanta kiwon dabbobi a kudu tamkar sayar da kayan gyaran motoci a Arewa.

Karin bayani akan: Garba Shehu, Yemi Osinbajo, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.

Bayan ‘yan kwanaki kuma Garba Shehu ya fitar da sanarwa, yana cewa matakan da gwamnonin suka dauka, suna da ayar tambaya ta fuskar doka, a madadin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Malam Garba Shehu, Kakakin shugaban Najeriya (Instagram/ Garba Shehu)
Malam Garba Shehu, Kakakin shugaban Najeriya (Instagram/ Garba Shehu)

To sai dai Bamgbose ya ce wannan ma "ai almara ce, a ce wai shugaban kasa ba zai iya Magana kai tsaye ga jama’arsa ba," wanda hakan in ji shi, ya nuna cewa babu tsari a fadar ta shugaban kasa.

Ya ce “yan Najeriya na cikin rudani akan wa ye ke tafiyar da shugabancin kasar nan.” Ya ci gaba da cewa kuma ‘yan Najeriya ba za su iya bambancewa da sa'adda Garba Shehu ya ke bayyana ra’ayin kashin kan sa ba, ko na shugaban kasa.

Akan haka ya yi kira ga shugaba Muhammadu Buhari da ya fito ya yi wa ‘yan Najeriya jawabi ba da bata lokaci ba, domin kuwa a cewar sa, “Garba Shehu bai da hujja a kundin tsarin mulki, na yin aiki a matsayin shugaban Najeriya.”

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na jagorantar taron kasashen yankin Tafkin Chadi a Abuja
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na jagorantar taron kasashen yankin Tafkin Chadi a Abuja

Dan gwagwarmayar ya ce “mutum ba yi kuskure ba idan ya ce muna da fadar shugaban kasa fiye da daya a Najeriya, kai, ta bayyana cewa muna da shugaban kasa fiye da daya a Najeriya.”

Ya bayyan mamakin yadda shugaba Buhari wanda ya zagayen duk fadin kasar a lokacin yakin neman kuri’un a zabe shi, amma kuma yake kin Magana kai tsaye ga jama’arsa, musamman a irin wannan muhimmin lokaci da ‘yan kasa suke shan ukubar kalubalen tsaro.

Masu fashin baki a Najeriyar dai sun dade suna sukar lamirin shugaba Muhammadu Buhari akan abin da suka kira “halin ko oho” ta hanyar rashin halarta ko kuma yi wa ‘yan kasa jawabin karfafa gwiwa, a duk lokacin da suka shiga wani mawuyacin hali.

Ko a farkon makon nan ma Buhari da mataimakinsa Yemi Osinbajo, sun fuskanci kakkausar suka akan kin halartar jana'izar marigayi babban hafsan sojin Najeriya, da wasu hafsoshi da jami'an soji 10 da suka ran su a hatsarin jirgin saman soji a Kaduna, duk kuwa da cewa suna a Abuja aka yi jana'izar.

XS
SM
MD
LG