Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Nzuko Umuna Ta Bukaci Babban Sufetan ‘Yan Sanda Ya Janye Umarnin Kashe 'Yan Kungiyar IPOB


DIG Usman Alkali Baba
DIG Usman Alkali Baba

Kungiyar kwararru mai fafutukar daidaita lamurran zamantakewar al’umma ‘yan kabilar Igbo mai suna, Nzuko Umuna, na neman babban sufetan ‘yan sandan Najeriya, Usman Alkali Baba, ya janye umarnin sa na jami’an ‘yan sanda su kashe duk wani dan haramtaccen kungiyar IPOB.

Kungiyar Nzuko Umuna ta bakin shugaban kwamitin shari’ar ta, Sam Amadi, ta yi Allah wadai da cigaba da afkawa jami’an tsaro da wasu miyagu ke yi a yankunan kudancin Najeriya inda ta bukaci gwamnati ta gudanar da bincike mai zurfi kan lamarin don gano ainihin masu aikata aika-aikar duba da irin manyan makamai da su ke amfani da su.

Shugaban kwamitin shari’ar kungiyar Nzuko Umuna, Sam Amadi, ya bukaci babban sufetan ’yan sandan Najeriya, Usman Alkali Baba, ya janye umarnin da ya bawa jami’ansa su kashe duk wani dan kungiyar IPOB da su ka gani don kare kan su abun da kungiyar ta ‘yan kabilar Igbo ta ce ya sabawa tsarin mulkin dimokuradiyya kuma zai iya jawo matsalar kashe mutanen da basu ji ba su gani ba a yankunan kudu din, ya na mai kira ga kungiyar kare hakkin bil’adama ta kasa ta duba wannan lamari.

Karin bayani akan: jihar Filato, Usman Alkali Baba, IPOB, Nigeria, da Najeriya.

A bangaren gwamnati, shugaban kungiyar gwamnonin arewa kuma gwamnan jihar Filato, Simon Lalong, ya ce daya daga cikin mafita ga matsalolin tsaro shi ne hukunta duk mai laifi ba tare da la’akari da kabila ko addininsa ba kuma ya bada matsayarsu kan matakin gwamnonin kudu.

A baya-bayan nan dai, matsalolin tsaro na kara ta’azarra a dukkan shiyoyin Najeriyaa kama daga kudu da ake zargin ‘yan kungiyar IPOB da kashe-kashen jami’an tsaro, arewa maso gabas da ayyukan ta’adanci, arewa maso yamma da ayyukan yan bindiga dadi sai kuma yammacin kasar da ake fafutukar neman kasar yarbawa lamarin da ke bukatar gwamnatin tarayyar kasar ta bullo da sabin dabarun samo mafita mai dorewa.

Saurari cikakken rahoton a sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:04 0:00

XS
SM
MD
LG