Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ghana Da Kenya Sun Cimma Yarjejeniyar Fahimtar Juna Don Kara Karfafa Alaka


Williams Ruto da Nana Akufo Addo
Williams Ruto da Nana Akufo Addo

Kasar Ghana da Kenya sun kara habaka huldar diflomasiya da tattalin arziki, ta hanyar rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna da za su tabbatar da hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu da burin nemo hanyoyin da kasashen za su bunkasa huldar kasuwanci, tattalin arziki da zamantakewa tsakaninsu.

ACCRA, GHANA - Kasashen biyu sun rattaba hannu kan wasu yarjeniyoyi 7 da suka hada da ilimi, yawon bude ido, tsaro, da inganta zuba jari, masana'antu, kere-kere da kasuwanci, daga cikin ziyarar kwanaki uku da shugaban kasar Kenya, William Ruto, ya kawo zuwa Ghana.

Shugaban kasar Nana Akufo-Addo da na Kenya, William Ruto, ne suka shaida yayin da Ministar harkokin wajen Ghana, Shirley Ayorkor Botchwey, da sakataren majalisar ministocin harkokin wajen Kenya, Dokta Musalia Mudavadi, suka jagoranci rattaba hannu kan yarjejeniyar diflomasiya a fadar shugaban kasa, Jubilee House, dake Accra.

Williams Ruto
Williams Ruto

Haka kuma an rattaba hannu kan wasu yarjeniyoyi da suka hada da ilimi, yawon bude ido, hadin gwiwar tsaro, kasuwanci da zuba jari, masana'antu da gudanar da mulki domin karfafa alakar dake tsakanin kasashen biyu.

A wani taron manema labarai na hadin gwiwa, shugaba Akufo-Addo ya ce, ‘Huldar kasuwanci da tattalin arziki tana ci gaba da bunkasa a tsakanin kasashen Ghana da Kenya, inda kasashen biyu ke kara fahimtar juna da kuma nuna goyon baya ga juna a kungiyoyin kasa da kasa da suka hada da MDD, Tarayyar Afirka, da kungiyar kasashen renon Ingila, na Commonwealth’.

Shugaba Ruto a nasa bangaren ya bayyana cewa, ‘yancin zirga-zirgar jama’a tsakanin Ghana da Kenya ya haifar da fa’ida sosai a fannin kasuwanci, zuba jari, da kuma yawon bude ido.

Williams Ruto da Nana Akufo Addo
Williams Ruto da Nana Akufo Addo

A dangane da haka, ni da mai girma shugaban kasa, mun lura cewa, kasuwanci tsakanin Kenya da Ghana na bunkasa a shekarar 2022, misali, a shekarar 2022, Kayayyakin da Kenya ta shigo da su Ghana sun kai dalar Amurka miliyan 10.4, kuma an kiyasta kayayyakin da ake shigo da su a kan dalar Amurka miliyan 4.8.”

Mai sharhi kan harkokin siyasar cikin gida da waje, Malam Issah Abdul Salam a tsokacinsa kan wannan alaka da aka dora tsakanin Ghana da Kenya yace, shugaba William Ruto ya zo Ghana ne don kara jaddada alaka mai kyau dake tsakaninsu tun da jimawa. Kuma wannan ziyarar da aka kara, ‘ilimi, yawon bude ido da ba da dama ga ziyarar kasashen juna, abubuwa ne da za su samar da mafani masu dimbin yawa tsakanin Ghana da Kenya”.

Jami'an gwamnatocin kasashen Kenya da Ghana
Jami'an gwamnatocin kasashen Kenya da Ghana

Masani kan harkokin kudi da kasuwanci, Hamza Attijjany, yace kasashen biyu za su amfana ta bangaren tattalin arziki, musamman a kasuwanci da babu shinge tsakanin kasashen Africa, da kasar Ghana da Kenya suka runguma da hannu biyu-biyu. Yace, ‘A lokacin da kasar Kenya ta fara yin batir, Ghana ce kasa ta farko da ta fara kawowa don kasuwanci. Lallai Ghana da Kenya za su samu ci gaban tattalin arziki da ma nahiyar Afirka baki daya’.

Al’ummar kasashen biyu, za su samu alfanu idan an tabbatar da wadannan yarjejeniyoyin, in ji mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, Malam Issah Mairago Gibril Abbas. Yace, daliban kasashen biyu za su samu damar zurfafa iliminsu ta hanyar yarjejeniyar; haka kuma ‘yan kasuwar kasashen za su ci moriyar shirin nan na cinikayya tsakanin kasashen Afrika mara shinge AfCFTA.

A cikin ziyarar shugaba Ruto na kwanaki ukun, ya ba da lekca a hedkwatar AfCFTA; ya ziyarci kabarin tsohon shugaban Ghana, Kwame Nkrumah, a Accra, kuma Ghana ta karrama babbar karramawa mai daraja, wato Companion of the Order of the Star of the Volta.

A sauraricikakken rahoton Idris Abdullah:

Ghana Da Kenya Sun Cimma Yarjejeniyar Fahimtar Juna Don Kara Karfafa Alaka.MP3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:49 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG