Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

GHANA: Farashin Kayayyaki Ya Haura Daga 19.4% Zuwa 23.6%


Kobina Annim, masanin kididdigar gwamnati a Ghana
Kobina Annim, masanin kididdigar gwamnati a Ghana

Mafi yawancin masu sana’a a Ghana sun ce hauhawan farashin kayayyaki yana karya musu jari.

Farfesa Kobina Annim masanin kididdigar gwamnati a Ghana ya ce yawan hauhawar farashin kayayyaki tsakanin watan Maris 2022 da Afrilu 2022 ya haura zuwa 23.6% daga 19.4%.

A wani taron manema labarai da aka gudanar a birnin Accra hukumar kididdigar ta bayyana farashin sufuri, kayan abinci da abin sha, da gidaje, ruwa, wutar lantarki, iskar gas da man fetur da sauransu yayi tashin gwauron zabi.

Yayinda mafi yawancin masu sana’ar a Ghana sun ce hauhawan farashin kayayyaki yana karya musu jarin.

Sarki Umaru Ashiru masanin tattalin arziki a Ghana yace idan farashin abinda ake sarrafa kayan da jamma’a ke saya yayi sama sai farashin kayan kuma yayi sama, haka kuma abinda jamma’a suka fi saya a kasuwa, amma ainihin matsalar ya danganta da faduwar darajar cidi wato kudin Ghana akan dala da kuma kayan da ake shigowa dasu daga kasashen waje.

Saurari cikakken rahoton Hauwa AbdulKarim cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:23 0:00
XS
SM
MD
LG