Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ghana Ta Sami Kason Farko Na Rigakafin Coronavirus


A karon farko kasar Ghana ta karbi alluran rigakafin coronavirus da ake samarwa ta hanyar shirin raba alluran rigakafi na bai daya a duniya da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ke kula da shi.

Wani jirgin sama dauke da allurai 600,000 na rigakafin AstraZeneca-Oxford na Jami’ar Oxford ya isa Accra babban birnin kasar a ranar Larba, a cewar wata sanarwar hadin gwiwa daga WHO da UNICEF, Asusun Bayar da Agajin Gaggawa na Yara na Majalisar Dinkin Duniya.

Cibiyar ta Serum ta Indiya, wace ita ce masana’antar rigakafi mafi girma a duniya, ita ce ta kirkiro allurar rigakafin.

An sayo alluran rigakafin da aka aika zuwa Ghana ta hanyar COVID-19 Vaccines Global Access Facility, ko COVAX, wanda wani shiri ne da hukumar WHO ta kaddamar tare da hadin gwiwar Hadakar Masu Yaki Da Annoba ta Coalition for Epidemic Preparedness Innovation, Gavi, da Gamayyar Masu Samar Da Rigakafi ta The Vaccine Alliance, da kungiyar da masu hannu da shuni ta Bill da Melinda Gates suka kafa don yiwa yara rigakafi a kasashe mafi talauci na duniya.

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Gobara A Jihar New York

An Yi Jana'izar Mutane 15 Da Suka Mutu A Gobara A Jihar New York
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG