Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sanda Sun Yi Wa Gidan Dino Melaye Kawanya


Gidan Dino Melaye zagaye da 'yan sanda
Gidan Dino Melaye zagaye da 'yan sanda

Bayan da aka sako Sanata Dino Melaye wanda aka tsareshi yau litinin a filin jirgin saman Nnamdi Azikwe yayin da zai je Morocco, 'yan sanda sun yi wa gidansa a Abuja kawanya.

"'Rundunar kwantar da tarzoma sama da 30 dauke da makamai sun yi wa gidana a Maitama Abuja diran mikiya. Sannan duk hanyoyin zuwa gidana an rufe ba shiga-ba-fita " inji Dino Melaye a shafinsa na twitter.​

Haka kuma ya wallafa cewa, 'yan sandar sun cafke dan uwansa da abokinsa a gaban gidansa din.

Kawo yanzu rundunar 'yan sanda ba su ce komai dangane da abun da ke faruwa ba.

A baya dai 'Yan Sanda na zargin Melaye da kin bayyana a gaban kotu don fuskantar shari'a, a bisa zargin da ake masa na daukar nauyin wasu bata-gari da mallakar makamai ba bisa ka'ida ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG