Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Giorgia Meloni Na Shirin Zama Mace Ta Farko Da Za Ta Rike Mukamin Firaminista A Italiya


Snap election in Italy
Snap election in Italy

Sai dai bisa al’ada, mika mulki a Italiya kan dauki tsawon makonni kafin a rantsar da sabuwar gwamnati.

Wata gamayyar jam’iyyu siyasa masu ra’ayin mazan jiya karkshin jagorancin jam’iyyar Brothers Party of Italy ta Giorgia Meloni na hangen yiwuwar lashe zaben majalisar dokokin kasar, kamar yadda sakamakon farko ke nunawa a ranar Lahadi.

Sakamakon farkon ya nuna cewa hadakar jami’yyun da suka hada da League ta Matteo Salvini da Forza Italia Party ta Silvio Berlusconi, sun samu kashi 41 da kashi 45 a zaben da aka yi.

Wannan na nufi sakamakon, ya isa jam’iyyun su samu rinjaye a majalisun dokokin kasar.

A ranar Litinin ake sa ran za a fitar da cikakken sakamakon.

Idan kuma har sakamakon ya tabbata, hakan na nufin Meloni, wacce jam’iyyarta ta samu kashi hudu cikin 100 a zaben 2018, a wannan karo za ta zamanto jam’iyya mafi girma a Italiya.

Kazalika hakan na nufin, a matsayin Meloni na shugabar wannan jam’iyya, dukkan alamu na nuni da cewa ita za a zaba a matsayin mace firaminista ta farko a Italiya.

Sai dai bisa al’ada, mika mulki a Italiya kan dauki tsawon makonni kafin a rantsar da sabuwar gwamnati.

Italiya na da tarihin kasancewa kasa mai fuskantar tarnaki a harkokin siyasanta, kuma firaministan da zai karbi mulki, zai zamanto wanda zai jagoranci gwamnati ta 68 tun daga shekarar 1946.

XS
SM
MD
LG