Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ruwan Sama Kamar Da Bakin Kwarya Ya Hallaka Mutane 10 A Italiya


Sauyin Yanayi A Italiya
Sauyin Yanayi A Italiya

Rahotannin sun ce akalla mutane 10 suka mutu yayin da wasu hudu suka bace bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi a tsakiyar kasar Italiya, lamarin da ya sa batun sauyin yanayi ya zama da muhimmanci mako guda kafin zaben kasar.

Ruwa ya ci garuruwa da kauyuka da yawa, lamarin da ya sa tituna suka zama tamkar koguna bayan da aka sheka ruwan sama na kimanin milimita 400 a cikin sa’o'i biyu.

A baya hukumomin bada agajin gaggawa sun ce mutune 7 ne suka mutu, amma adadin ya karu zuwa 10 da hantsi, kamar yadda kamfanin dillanci labarai na AGI ya fada, inda ya ambato hukumomin yankin.

Cikin wadanda aka samu rahoton bacewarsu har da karamin yaro a cikin wata mota. An iya kubutar da mahaifiyarsa amma ruwa ya tafi da yaron, a cewar AGI.

Hukumar kashe gobara ta ce jami'anta 300 na aiki kan ambaliyar, sannan an ceto mutane da dama a cikin daren Alhamis bayan da suka fake kan soron gidajensu da kuma kan bishiyoyi.

Wurin da ya fi muni shi ne Ancona, wani birni mai tashar jiragen ruwa da ke yankin tekun Adriatic, inda aka samu katsewar hanyoyin lantarki da waya a wurare da dama. An rufe makarantu a yankunan da abin ya shafa ranar Juma’a.

Titunan garin Senigallia da ke daura da gabar tekun yankin sun zama koguna, yayin da hotunan da aka dauka ta sama a kauyen Pianello di Ostra suka nuna tituna cike da tabo, motocin da ruwa ya tafi da su kuma jibge a wuri guda.

Wannan bala'in dai ya faru ne 'yan kwanaki kadan gabanin babban zaben kasar da za a yi ranar 25 ga watan Satumba, kuma ‘yan siyasar kasar daga jam'iyyu dabamdaban sun jajanta wa wadanda abin da ya shafa.

XS
SM
MD
LG