Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Girgizar Kasar Italiya Ta Hallaka Mutane 247 da Raunata Wasu 360


Dubban gidaje suka rugurguje baicin rayuka da suka salwanta

Alkalumman asaran da aka yi a sanadin gagarumar girgizan kasan da ta abkawa kasar Italiya jiya Laraba, na nuna cewa mutane akalla 247 ta hallaka, ta raunana wasu kamar 360.

A yau ne Firayim Ministan kasar, Matteo Renzi, ya zagaya yankin da abin ya fi shahuwa ta jirgin sama, daga baya ya sauko ya gaggaisa kuma ya jajanata wadanda abin ya shafa, kafin ya gana da ministan samarda aiyukka da abubuwan more rayuwa na kasar

Sai dai Firayim Ministan din yaki yin magana da manema labarai, inda yace lokacin “maganar baiyi ba.”Da misalin karfe 3.30 na dare ne dai girgizan kasan da ta abkawa yankin dake tsakiyar Italiyar, inda kuma tayi barna a garuruwa da dama.

Masu aikin ceto suna zakulo mutane daga baraguzen gine gine
Masu aikin ceto suna zakulo mutane daga baraguzen gine gine

Akwai yara kanana da ama daga cikin wadanda suka rasa rayukkan nasu a cikin al’amarin. Hukumar Kiddidigar Yanayi ta Amurka ta ce karfin girgizan ya kai karfin awon 6 da digo 2, kuma yankin ta bazu akansa ya kai da’irar kamar kilomita 10.

XS
SM
MD
LG