Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gobara Ta Barke a Gidan Namun Daji Na London


Gobara ta barke a gidan ajiye dabbobin daji na birnin London, inda wani ma’aikaci ya sami rauni yayin da kuma wata dabba mai dogon hanci da ake kira aardvark ta mutu.

Haka kuma wasu dabbobi hudu masu kama da kurege da ake kira meerkat sun bace, kuma ake tunanin sun mutu dalilin gobarar, a cewar jami’an gidan ajiye namun dajin.

Sama da ‘yan kwana-kwana 70 da manyan motocin kashe gobara 10 ne suka kwashe kusan sa’o’i uku kafin su kashe gobarar.

Ya zuwa yanzu dai ba a san abin da ya haddasa gobarar ba.

An baiwa ma’aikatan gidan namun dajin takwas kulawar nan take, saboda sun shaki hayaki.

Shi dai gidan namun dajin na London yana dauke da dabbobi sama da 20,000, kuma yana cikin shahararren wajen shakatawar nan na Regents Park wanda ke birnin London, inda masu yawan bude ido kimanin miliyan 1.2 kan ziyarci wurin duk shekara.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG