Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gobara Ta Kashe Mutane 150 A Lokacin Da Suke Kwasar Man Fetur


File photo

Jami’ai a Sudan ta Kudu sun ce a kalla mutane 150 ne suka mutu, lokacinda suke kokarin tarbar man fetur daga wata motar dakon mai da ta fadi.

Da farko jami’ai sunce mutane tamanin da biyar ne suka mutu, a hadarin da ya auku ranar laraba, sai dai yau jumma’a adadin ya haura ainun. Gobarar ta auku ne a kan wata hanya dake kusa da garin Maridi, mai tazarar kilomita dari biyu da hamsin da Juba babban birnin kasar.

Mariam Tito, shugabar lardin Mambe Mayan ta shaidawa wani shirin Muryar Amurka “South Sudan In Focus” cewa, mai yiwuwa ne adadin wadanda suka rasu ya karu kasancewa mutane da dama sun yi mummunar kuna.

Irin wannan fashewar tana yawan aukuwa a kasar ta gabashin Afrika da talauci ya yiwa katutu, inda mutane suke dafifi idan motar dakon mai tayi hadari,suna satar mai. A watan Yuni shekara ta dubu biyu da goma sha uku,, mutane talatin suka mutu a wata gobarar motar dakon mai a kasar Uganda.

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG