Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Ahmed Ibrahim Lawan, ya fada wa Muryar Amurka cewa ya na da tabbacin cewa Shugaba Muhammadu Buhari zai sa hannu a Kasafin kudin shekarar 2020 gobe Talata, 17 ga watan nan na Disamba.
Majalisar dokokin kasar ta yi kari akan kasafin da Shugaba Buhari ya tura mata daga Naira Triliyan goma da digo uku (10,330,416,607,347) zuwa Triliyan goma da digo biyar (10,594,362,364,830).
Majalisun duka biyu, sun amince da Kasafin tare da fatan za a fara aiwatar da shi daga watan Janairun shekarar 2020 zuwa Disamban shekarar sabanin yadda ake yi a baya.
Sanata Ahmed Lawan, ya ce Majalisar ba 'yar amshin Shata ba ce, jituwar da ke tsakaninta da bangaren gwamnati na nuni da cewa Majalisar ta na bin umurnin mazabu ne tare da yi wa al’ummar Najeriya aiki. Kuma duk abin da suka yi, babu wanda ya saba wa doka.
Ga rahoto ckin sauti.
Za ku iya son wannan ma
-
Maris 02, 2021
Mayakan Boko Haram Sun Fice Daga Garin Dikwa Na Jihar Borno
-
Maris 02, 2021
An Sako Daliban Makarantar Jangebe
-
Maris 02, 2021
Gwamnatin Jihar Yobe Ta Ba Da Umarnin Rufe Makarantun Kwana
-
Maris 02, 2021
'Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 10 A Jihohin Kaduna Da Sokoto
-
Maris 02, 2021
DSS Ta Saki Salihu Tanko Yakasai
Facebook Forum