Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Google Ya Kaddamar Da Shirin Ba Da ‘Data’ Kyauta a Lagos


Matasa a wajen ginin da aka kaddamar da cibiyar shirin Google na data kyauta.
Matasa a wajen ginin da aka kaddamar da cibiyar shirin Google na data kyauta.

Cikin makon nan ne kamfanin sadarwa na Google ya kaddamar cibiyar shirin ba da data kyauta a Najeriya, karkashin wani tsari da ake yiwa lakabi da 200 Wi-Fi hotspots.

Shirin wanda aka kaddamar a jihar Lagos, ya shigar da Najeriya cikin jerin kasashen duniya hudu masu cin gajiyar tsarin na kamfanin Google, amma ta farko a nahiyar Afrika.

Manufar tsarin dai shi ne saukaka yanayin karba ko aika sakonni ta kafar sadarwar intanet a tsakanin ‘yan Najeriya, musamman dalibai, ma’aikatan harkokin yada labarai masu bincike da kuma ‘yan kasuwa da sauran ma’abota amfani da kafar sadarwar intanet.

Baya ga aikawa da karbar sako cikin sauki da kuma rahusa, masu kula da al’amura na ganin matakin na kamfanin Google na ba da data kyauta wani kalubale ne ga kamfanonin sadarwa a Najeriya wadanda aka dade ana korafi kan rashin ingancin ayyukansu.

Gabanin kaddamar da tsarin na ba da data kyauta ga masu amfani da Intanet, kamfanin da Google ya kaddamar da irin wannan tsari a kasashen India, Indonesia, Mexico da kuma Thailand.

Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Mahmud Ibrahim Kwari.

please wait

No media source currently available

0:00 0:05:09 0:00

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG